Karuwar hare-haren bam a Pakistan | Labarai | DW | 02.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar hare-haren bam a Pakistan

Rahotannin daga Pakistan na cewar wasu bama-bamai biyu sun tarwatse a wajen ginin wata kotu da ke Mardan a arewacin kasar lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane da damar gaske.

Masu aiko da rahotanni suka ce daga cikin wanda suka samu raunukan har da jami'an tsaro da kuma lauyoyi wanda wasunsu ke cikin halin rai kwakwai-mutu kwakwai. Ya zuwa yanzu dai ba wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan hari wanda ke zuwa jim kadan bayan wani makamanci da wata kungiya da ke da alaka da Taliban ta kai wata unguwa da Kiristoci da dama ke zaune.

A 'yan makonnin nan Pakistan ta fuskanci hare-haren bam da ake alakantawa da kungiyoyi masu akifin kishin addini kuma hakan na zuwa ne daidai lokacin hukumomi a kasar ke cigaba da matsa lamba wajen kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda ciki kuwa har da IS da ke rajin girka daular Islama.