1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fuskantar hatsuran jiragen sama?

Muhammad Bello AH
November 15, 2023

A na samun karuwar fargaba ga ma su tafiye-tafiye ta jiragen sama a Najeriya bisa la'akkari da yawaitar hadduran jiragen musamman a baya-bayan nan, da a ka samu haddura har sau uku cikin sati biyu a kasar.

https://p.dw.com/p/4YqYu
Hoto: George Osodi/AP Photo/picture alliance

 

 Hukumomin kamfanonin jiragen na sama dai sun danganta wadannan haddura da sauyin yanayi na damina. Hadarin jirgin na sama dai na baya-baya  nan shi ne da ya afku a filin sauka da tashi na Omaga da ke Fatakwal jahar Rivers da ya afku.

Barazanar faduwar jiragen sama a Najeriya saboda yaayin damina

Nigeria | Murtala Muhammed International Airport
Hoto: Osodi Emmanuel/IMAGO

Wani hadarin jirgin sama samfurin CRJ 900 Bombardier,mai rajista  5N-BXR da ya afku a filin sauka da tashin jiragen sama na Omagwa jihar Rivers, in da jirgin ya zame daga ainihin titin saukarsa,da kuma aka nunar mutane da dama sun dan jikkata,al'amari ne da ya fara sa fargaba ga ma su tafiye-tafiye ta jiragen na sama a Najeriya, bisa ma lakkari da cewar, hadarin na jirgin sama, karo na uku ke  nan cikin sati biyu das u ka gabata. Bayan wannan hadarin dai, akwai na jirgin Boeing 737 Jet,mallakin Aero Contaractor, da shi kuma ya yi sauka mai kada hantar matafiya,ya kuma zarce iyakar titin da ya kamata ya tsaya a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sai kuma na wani jirgi HS25BHS25Bda ya yi  saukar ta bazata.

Harkokin jiragen sama a Najeriya, masana na cike da dimbin kalubale

Nigeria | Murtala Muhammed International Airport
Hoto: Osodi Emmanuel/IMAGO

 A watannin baya dai,an ta yawo da wani faifan bidiyo a Najeriyar, da ya nuna yadda a ka samu wasu bata gari a kasar, sun dau matakin fara yin algus a man da jiragen na sama ke amfanin da shi, inda a ka ringa ganin ruwa a ciki, inda da daman jama'ar kasar, musamman ma ma su tafiye-tafiye ta jiragen na sama, suka yi ta yin Allah wadai, tare ma da kira ga hukumomin kasar na su sake tashi tsaye kan haka, domin samar da tsaro ga jiragen da ma kayayyakin da su ke amfani da su. Harkokin jiragen sama dai a Najeriya, masana sun nunar na cike da dimbin kalubale, da su ka hada da na tangaltangal din da tattalin arzikin Najeriyar ke yi a halin yanzu,da karancin kudaden tafi da harkar ,inda ma katutun basuka ke yi musu shan kai,sannan da daman filayen jiragen na sama a kasar ,na bukatar gyara na  hakika.