Karin ilimi a kan sha′anin kiwon lafiya tsakanin Masar da Najeriya | Zamantakewa | DW | 24.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Karin ilimi a kan sha'anin kiwon lafiya tsakanin Masar da Najeriya

Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke a Labai Najeriya ta kulla yarjejeniyar da jami'ar Mansura ta Masar domin yin cudanya a fannin aikin likita.

Ägypten Kairo Proteste Verletzte (picture-alliance/dpa)

Musanya ta dalibai daga jami'o'i a fannin kiwon lafiya daga wata jami'a zuwa wata jami'ar don karin ilimi ya kan taimaka sosai wajen samun kwarewa da kuma kara fahimta a daidai lokacin da sabbin na'urori na kula da sha'anin kiwon lafiya ke kara bazuwa a duniya. Wannan yarjejeniya da jami'o'in biyu suka kulla za ta bai wa daliban kasashen damar daukar ilimi a Najeriya da Masar, abin da zai taimaka wajen kawo ci-gaba ga sha'anin kiwon lafiya a kasashen biyu.

Sauti da bidiyo akan labarin