Nijar: Rashin filayen kiwo babbar matsala ga makiyaya
April 5, 2019Talla
Daman dai matsalar canjin yanayi da kuma girma da garuruwa ke yi na sa da sannun a hankali ana rasa wasu filayen da makiyaya ke yin amfani da su don kiwo.To amma hali na baya-baya nan da ake fuskanta a Nijar na yadda masu kudi ke mallake filayen ta hanyar sayesu ya sa al'amuran kiwon cikin wani mummunar hali.Tuni dai kungiyoyin farar hula suka nuna fargabansu a game da karancin filayen kiwon.