Kara jibge sojin Amirka a tekun fasha | Labarai | DW | 21.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kara jibge sojin Amirka a tekun fasha

Gwamnatin Amirka ta bayyana matakin kara jibge sojojinta a yankin Gulf, kwanaki bayan kai wani hari kan matatan man fetir din Saudiyya da kasashen biyu ke zargin Iran da hannu wajen kai wa a makon da ya gabata.

A yayin da yake ganawa da manema labarai sakataren tsaron Amirka Mark Esper, ya bayyana cewa matakin jibge sojan shi ne na farko, kana kuma Amirka da kawayenta na iya kara daukar wasu muhimman matakai daidai gwargwadon yadda matsalar ta ke tafiya a yankin. Ko baya ga matakin na kara jibge jami'an tsaron Amirka a yankin, Shugaban Amirka Donald Trump ya kuma kara tsaurara takunkumi mafi tsauri ga babban bankin kasar Iran, matakin da ke a matsayin irinsa na farko da Amirka ta taba kakabawa kan wata kasa ta ketare.