Kara faduwar darajar Naira a Najeriya | Siyasa | DW | 23.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kara faduwar darajar Naira a Najeriya

Bayan share wata da watanni yana kokarin kare Naira, a ranar Litinin ce babban bankin Najeriya na CBN ya kaddamar da sabon shirin dora Nairar kan turba irin ta kasuwa.

Bayan shelar ganin an sakar wa kudin Najeriya mara a fagen kasuwanci da kudaden ketare, a iya cewa tun daga lokacin rawa ta sauya salo musamnman ta fannin cinikaiya a tsakanin 'yan kasar.

Gwamnati dai ta tabbatar da cewa tana bukatar akalla Dalar Amirka miliyan dubu hudu a wani mataki na cimma manufar da aka sanya a gaba.

A waiwaye adon tafiya kuwa gwamnan babban bankin kasar Mr. Godwin Emefiele ya ce bankin zai shiga cikin hada-hadar kudade a kasar da nufin sanya halin da'a.

Yana mai cewa bankin kasar zai shiga cikin kasuwancin kudaden ketare daga lokaci zuwa lokaci idan har hakan ta taso. To abin tambaya a nan shi ne, ko yaya farashin Naira yake a kasuwar a yanzu?

Bincike dai ya nuna cewa kasuwar sanya hannayen jari a Najeriya cike take da karsashi baya ga manya da kanannan 'yan kasuwa. Mr Adedipe John masani ne a fannin hada-hadar kudade a Najeriya.

Ya ce: "Ko shakka babu wannan sabon tsarin na gwamnatin Najeriya wani mataki ne na farfado da darajar Naira da kuma fannin fitar da kaya da shigowa da su cikin kasa domin habaka arzikinta.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin