Kano: Tsugune ba ta kare ba dangane da kirkiro karin masarautu | Siyasa | DW | 13.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kano: Tsugune ba ta kare ba dangane da kirkiro karin masarautu

A jihar Kano ana ci gaba da cece kuce tun bayan rattaba hannu a kan dokar kara masarautun gargajiya guda hudu a Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ba ta mayar da martani kan batun kirkirar karin masarautu a Kano ba

Fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ba ta mayar da martani kan batun kirkirar karin masarautu a Kano ba

Mutane da dama a Kano na fassara matakin da gwamnatin jihar ta dauka na kirkirar karin masarautu hudu a matsayin wata ramuwar gayyar siyasa tsakanin gwamna ga mai martaba Sarkin Kano wanda kuma ya jawo al'amura marasa dadi a jihar.

A ranar Lahadi Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II ya dawo gida bayan ziyara da ya kai kasashen waje. Yayin dawowar tasa dai ya sami tarba daga dubban mutane lamarin da ke nuna cewar wannan mataki da ake dauka tamkar yana kara masa farin jinni ne.

Wannan tarba da Sarkin na Kano ya samu dai ta bayar da mamaki matuka musamman ganin yadda wasu ke ganin cewar an yi dokar kirkirar karin masarautun ne da wata nufaka ta siyasa. Sai dai kuma sakataren gwamnatin Kano Malam Usman Alhaji ya ce ko kadan babu wata nufaka a kan wannan batu na kirkirar karin sarakunan yanka a Kano.

Mai Girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Mai Girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Sai dai kuma wannan mataki na kara sarakunan yankan ya fara fuskantar tazgaro domin tuni wata babbar kotu a Kano ta dakatar da yunkurin har sai an zo gabanta, haka kuma yanzu wasu masarautun sun fara nuna kin amincewarsu da wannan sauyin fasali wanda suka ce ya jirkita tarihi da asali kamar yadda wakilan masarautar Wudil da aka mayar karkashin sabuwar masarautar Gaya suka bayyana, suna masu cewar ba za su yi wa sarkin Gaya mubaya'a ba.

Ga manazarta irin su Dr Maude Rabiu Gwadabe wannan mataki na keketa masarauta abu ne da zai ci gaba da jawo farin jini ga Sarki Muhammadu Sanusi II.

Wani abu da shi ma aka bude shafinsa a kan wannan batu na kirkirar sarakunan yanka shi ne yadda ake tura 'yan daba su tarwatsa duk wani taro da ka iya zama taron kin jinin wannan mataki. Alal misali an shirya taron sama wa Kano mafita a gidan Mabayya, 'yan daba da makamai sun tarwatsa taron haka kuma 'yan daba sun tashi zanga-zangar lumana da wasu matasa suka shirya.

Yanzu dai kallo ya koma kotu domin ganin yadda za ta kaya biyo bayan yadda gwamnati ta ki bin umarnin kotu na dakatar da wannan mataki.

Sauti da bidiyo akan labarin