1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba Covid-19 ce ke kashe mutanen Kano ba

April 27, 2020

A jihar Kano ta Najeriya mahukunta sun ce mace-macen da ake yawan samu a 'yan kwanakin nan ba coronavirus ce ke haddasa su ba.

https://p.dw.com/p/3bSAn
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

Wannan bayani na gwamnatin Kanon ya biyo bayan rahoton da wata jarida a kasar ta bayar na cewa akalla mutum 150 ne suka mutu cikin kwanaki kalilan a birnin Kano. Sai dai wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa mutanen sun mutu daga cututtuka irinsu hawan jini da ciwon suga da sankarau da kuma maleriya, tana mai jaddada cewa ba corona ce ta kashe mutanen ba.

Jihar ta Kano dai na da mutum 77 masu coronavirus a cikin mutane 1,273 da suka kamu da cutar a kasar, a cewar hukumar NCDC mai yaki da cututtuka a kasar. 

Jihar Kaduna da ke makwabtaka da jihar Kanon ta sanar cewa ta kara wa'adin kwanaki 30 na jama'a su ci gaba da zama a gida ba tare da sun fito waje ba, don gudun kada cutar corona ta bunkasa a jihar kamar yadda ake gani a jihar Kano da Abuja shelkwatar Najeriya.