Kamarun: Mutane 79 sun mutu a hadarin jirgin kasa | Labarai | DW | 24.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamarun: Mutane 79 sun mutu a hadarin jirgin kasa

Hadarin jirgin kasa da ya afku a ranar Juma'a da ta gabata a kasar Kamarun, ya haddasa mutuwar mutane kusan 80 tare da jikkata wasu 551.

Shugaban kasar Kamarun Paul Biya ya kaddamar da zaman makoki na kasa baki daya bayan da ya dawo daga wani bulaguro na tsawon wata guda, inda jim kadan bayan saukarsa daga jirgi ya yi bayani inda yake cewa:

"Tunani na da kuma kalamai na farko, na yi sune zuwa ga iyallan wadanda wannan hadari ya rutsa da su da kuma wadanda suka jikkata. Sannan ina mai isar da gaisuwata ta ta'aziya zuwa garesu baki daya tare da fatan Allah ya bai wa wadanda suka ji raunuka sauki."

Adadin baya-bayan nan na wadanda suka rasu a hadarin jirgin kasan kasar Kamarun ya kai na mutun 79 a cewar tashar gidan radion kasar ta Kamarun ta CRTV. A ranar Lahadi ma dai an samu gano wasu gawawaki 11 abun da ya kai adadin ga mutanen 79. gdan radion ya sanar cewa akwai wasu mutane 551 da suka samu raunuka sakamakon hadarin inda mafi yawansu aka fice da su ya zuwa birnin Douwala, wasu kuma zuwa Yaounde domin kula da lafiyarsu.