Douala ne cibiyar kasuwancin Kamaru, kuma birnin da ya fi yawan al'umma a kasar. Ya kunshi babbar tashar jirgin ruwa da kasashe da dama ke amfani da ita.
Shi ne ya kasance babban birnin Kamaru na farko bayan shigowar Turawan mulkin mallaka na Jamus. Sannan ya ci gaba da zama inda aka fi harkokin saye da sayarwa. Ana cudeni in cudeka tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban a wannan birnin.