1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar mallakar muhalli a Kamaru

September 14, 2021

Tsawon shekaru al'umma da ke yankunan karkara ke tururuwa zuwa manyan birane a kasar Kamaru domin neman ayyukan yi da ma samun kudaden da za su iya mallakar gidajensu.

https://p.dw.com/p/40KIu
Kamerun Gericht Bamoun, Njapshe
Hoto: DW/H. Fotso

To sai dai a dalili na karancin filayen gini mutane kan fada hannun bata gari da kan gudu da kudadensu, yayin da su kuma masu gidajen kan wayi gari an rushe nasu gidajen.

'Yan kasar Kamaru musamman daga manyan garuruwa irin su Douala da ke zama cibiyar kasuwancin kasar da kuma Yaounde fadar gwamnati na fatan wata rana su sami arzikin mallakar muhalinsu. To sai dai duk yadda suka yi tanadi wannan buri na su kan ci karo da kalubale da kan hana shi cika, a sabili da yadda wadannan garuruwa ke kara tasowa.

Wannan dalilin ya bar wawason filayen tsakanin talaka da kuma attajirai da ke da kumbar susa. A nasu bangaren masu saiyar da filayen ganin yadda kowa ke da bukata sai su sayar da fili daya ga mutane da yawa, musamman ma ga wadanda basu da lokacin tantance filin da ba shi da wata matsala.

Birnin Douala
Hoto: DW/F. Muvunyi

Wannan matsala ta yi kamari a Douala da ke samun tururuwar al'umma masu hada hadar saye da sayarwa, birnin da ke da sama da al'umma miliyan 3 da dubu dari bakwai wanda kuma yawansu ke kara karuwa a kullum. Glory Wirkom Nyudze da ke zama malamar makaranta na daga cikin mutanen da ke fatan ganin sun mallaki muhallinsu a wannan birni.

Shekaru bayan tanadin taro da kwabonta ta kai ga gina gidanta to sai dai bayan kwashe shekaru a cikin gidan aka rushe mata shi ba tare da sanar da ita ba balle ta kai ga kwashe kayanta, wannan lamari ya kai iyalinta shiga cikin wani matsanancin hali.

"Bayan kwashe shekaru biyu zuwa uku a cikin gidan, muna zaune wani mutum ya fada mana wai mun yi mishi gini a kan filinshi, da farko mun dauka wasa yake yi sai daga baya muka ganshi da jami'an tsaro da ma'aikatan ma'aikatar gine-gine, kafin ka ce kwabo an rushe mana

Lauya Nkwamah Limen da ya kware a harkar sayen gidaje da filaye, na mai kira ga al'umma da su bi hanyoyin da suka dace a duk lokacin da suke da bukatar sayen filaye ko ma gida domin guje wa irin wannan matsalar.

BirninnYaounde
Hoto: AFP/Getty Images/M. Longari

 

"Idan har fili ya fada a kan mallakin gwamnati, to akwai kwamitin gwamnati da ke da alhakin kula da shi, kuma ire-iren wadannan filayen ba a samun shi ga mutanen da aka haifa bayan shekarar 1974, wannan doka ce a kan ire-iren filayen da gwamnati ta fidda. Filayen da ba na gwamnati ba kuma suna da takardu na musamman shi ma akwai dokar da ta tabbatar da hakan. Kuma akwai mutanen da ke da alhakin tabbatar da sahihancin ire-iren wadannan filayen. Ya kamata idan mutum zai sai fili ya tabbatar tsabtatace ne bashi da wata matsala"

 

Yanzu haka dai mahukunta a kasar ta Kamaru na kokarin magance wannan matsala ta karancin matsugunnai a manyan biranenta, inda ta fara gina gidajen gwamnati masu sasaucin kudi. Sai dai duk da maraba da wannan mataki da al'umma suka yi, matakin ya kasa taka rawa a kasuwar saida gidaje wanda hatta gidajen da gwamnati ke yi don talakawa su sami sauki masu hannu da shuni ne ke wawushewa.