Yaounde ko Yawunde ke zama babban birnin Kamaru, kuma birni na biyu mafi girma a kasar bayan Douala.
Ana yi wa Yaounde kirari da birni mai tuddai bakwai saboda wasu tsaunuka bakwai masu tarihi da suka kewayeshi. Ya kunshi mutane kusan miliyan uku. Kananan hukumomi biyar ne ke babban birnin na Kamaru, baya ga cibiyoyin kanfanoni da kafofin watsa labarai da dama.