Kamaru ta tarwatsa masu zanga-zanga | Labarai | DW | 22.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta tarwatsa masu zanga-zanga

'Yan sanda a birnin Douala na Jamhuriyar Kamaru sun tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar.

Madugun Adawar Kamaru Maurice Kamto

Madugun Adawar Kamaru Maurice Kamto

Jama'a dai ta yi jerin gwano a titunan Douala, inda wasu suka rike tutar Kamaru, suna fadin kalamai munana kan gwamnatin Shugaba Paul Biya.

Tun da farko madugun adawar kasar Maurice Kamto  ya kira zanga-zangar domin matsawa gwamnati lamba ta tsagaita wuta a rikicin 'yan awaren kasar da kuma kawo sauye-sayue a hukumar zaben kasar. 

To sai dai kuma masu zanga-zangar sun sha da kyar bayan da jami'an tsaro suka watsa musu hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su. Kazalika akwai wasu wadanda suka shiga hannun jami'an tsaron a matsayin masu kunnen kashi.