1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta hallaka mayakan Boko Haram 40

June 1, 2014

Sojojin kasar Kamaru sun hallaka 'yan Boko Haram yayin artabu cikin yankin arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/1CAEN
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jami'an tsaron kasar Kamaru sun hallaka tsageru 40 da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne yayin wata arangama cikin yankin arewacin kasar. Wata majiyar fadar shugaban kasar ta ce an yi dauki ba dadin a yammacin garin Kousseri da ke iyaka da Najeriya da kuma Jamhuriyar Chadi.

Gidan rediyon kasar ya ba da labarin jim kadan bayan an sako limaman Kirista 'yan kasar Italiya biyu da wata 'yar kasar Kanada wadanda aka sace a kasar ta Kamarun. Mutanen uku an sace su ne a arewacin kasar Kamarun watanni biyu da suka gabata.

Kamaru wadda ake gani ba ta taimaka wa Najeriya sosai wajen yakan 'yan Boko Haram masu dauke da makamai cikin wannan mako da ya gabata ta tura sojoji 1,000 domin tunkarar matsalar da mayakan masu kaifin kishin addinin Islama.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal