1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Ba mu kori 'yan hijirar Najeriya ba

Abdul-raheem Hassan
September 28, 2017

Hukumomin Kamaru sun kare kan su daga zargin da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Right Watch ta yi, na cewa sun tilasta wa 'yan gudun hijirar Najeriya sama da 1,000 komawa inda suka fito.

https://p.dw.com/p/2kqa2
Kamerun Flüchtlingslager Minawao
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kalubalanci kasar Kamaru da daukar matakin neman sake jefa rayuwar 'yan gudun hijirar Najeriya cikin hatsari na tilasta musu komawa yankunan da ba shi da tabbas na cikakken tsaro ganin yadda ya sha fama da rikicin Boko Haram, matakin da kungiyar ke ganin ya saba wa ka'idojin MDD na kare 'yan kudun hijira.

kakakin gwamnatin na Kamarun Issa Tchiroma Bakari, ya ce wannan zargi ba shi da tushe balle makama inda ya ce a yanzu haka kasar kamaru na kula da 'yan gudun hijira 500,000 daga sassa daban-daban na duniya.

Ya kuma kare zargin da ake yi wa sojojin Kamaru na gallaza wa 'yan gudun hijira da kuma tuhumarsu da aikata fyade, kakakin gwamnatin ya ce dukkanin sojojin kasar suna da horo a kan ayyukansu kuma suna mutunta dokoki.