1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama ta kaure bayan daure magoyan Kamto

Zakari Sadou RGB
December 28, 2021

Takaddama ta barke a Kamaru a sakamakon hukuncin dauri da wata kotun kasar ta yanke wa wasu magoya bayan madugun adawan kasar Maurice Kamto.

https://p.dw.com/p/44v5j
Kamerun Douala | Hotel Moise Kamto
Hoto: Henri Fotso

Kotun sojin Yaounde a kasar Kamaru ta yanke hukuncin dauri kan magoya bayan madugun ‘yan adawar kasar Maurice Kamto su 47 haka kuma ita kotun ta wanke wasu dalibai uku da aka zarga da yada sakon mayakan Kungiyar Boko Haram. Hukunce-hukuncen sun kama ne daga daurin shekara 1 zuwa 7 a gidan yari, kamar yadda wani kusa a jam’iyyar adawa MRC ta Maurice Kamto ya sanar. 

Wadannan mutane 47 da aka yanke wa hukuncin daurin, ana tsare da su tun ranar 22 ga watan Satumban shekarar 2020, lokacin da jam’iyyarsu da wasu jam’iyyun adawa suka shirya zanga-zangar adawa da Shugaba Paul Biya wanda ke kan karagar mulkin kasar ta Kamaru na tsawon  shekaru 39.

Kamerun Wahlen Paul Biya
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: AP

A wancan lokaci, ‘yan sanda sun yi amfani da karfi domin tarwatsa tarzomar musamman wanda ya gudana a birnin Douala, inda suka cafke sama da mutane dari biyar, kuma yanzu haka dari dari da ashirin da hudu, daga cikinsu na tsare, a cewar jam’iyyar ta MRC.

Wannan hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da madugun 'yan adawan Kamaru Maurice Kamto  yayi amfani da wannan damar da yake Kamaru ce ke da nauyin hada gasar cin kofin Afirka da kira ga gwamnatin Paul Biya da ta sako 'ya'yanta da aka garkame sai dai hakan ya ci tura. Lamarin da fusata 'yan siyasan kasar.

Yan Jam'iyyar MRC na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga gwamnatin Kamaru saboda yadda suke kalubalantar yanayin tafiyar da kasar da Shugaba Paul Biya ke yi da suka ce, ba bisa ka'ida ba duk da matsin lamba da yake sha daga kasashen waje dama kungiyoyin agaji ta kasa da kasa.

A bangare guda kuma kotun sojin Yaounde ta wanke dalibai uku da ake zargi da yada sakon mayakan Kungiyar Boko Haram da aka tsare tun ranar 14 ga watan Janairun 2015 daga bisani a yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a ranar 2 ga watan Nuwamba 2016 kamar yadda Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta sanar.