Kalubalen raya kasa ta Jamus a Najeriya | Siyasa | DW | 10.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen raya kasa ta Jamus a Najeriya

Sakamakon rikicin Boko Haram da Najeriya ke fama da shi, ministan raya kasa na Jamus zai duba ayyukan da kungiyoyinsu za su gudanar baya ga batun tattalin arziki.

Kungiyoyin raya kasa na Jamus na ci gaba da gudanar da ayyukansu a Najeriya duk kuma da matsalar tsaro da wannan kasa ke fuskanta. Hasali ma dai wadanda suka kudufa a arewacin kasar suna cikin barazanar rasa rayukansu sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke yawaita kai wa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar kungiyoyin kare hakkin dan Adam, mutane dubu uku ne suka rasu kayukansu a cikin shekaru hudu na baya-bayanan a tarayyar ta Najeriya sakamakon fafutuka da Boko Haram ke yi da makamai. Hakazalika mutane dubu 250 na rayuwa cikin fargabar tashin hakali a kauyukan da suka kewaye birnin Maidiguri na jihar Borno. Rikicin addini da kasar ta yi kaurin suna a kai ya saba shafar miliyoyin 'yan Najeriya.

Nigeria Anschlag in Jos 20.05.2014

Jami'an agaji na fuskantar matsala wajen ceto rayuka

A wannan yanayi ne Kungiyar Misereor ta Jamus ta ke kokarin samar wa al'umma ruwa mai tsafta. Sai dai kuma maimakon aikawa da jami'anta don gudanar da wannan aiki, kungiyar ta 'yan Katolika tana hada gwiwa ne da abokan huldarta na garuruwan da abin ya shafa don cimma burin da ta sa a gaba.

Su dai jami'an agajin suna fuskantar kalubale na sacesu da aka saba yi a Najeriya domin neman diyya. Sannan kuma rashin kyawun hanyoyin na zame musu karfen kafa, a cewar Matthia Kamp na kungiyar Misereor:

"A wasau lokutan ana rasa motar da za yi zirga-zirga da ita daga wannan gari i zuwa wancan. Mutane da dama na yin jigilar ne a kan babur. Ga shi kuma a wasu gurare an haramta a caba saboda 'yan Boko Haram na amfani da babura wajen kutsawa kauyuka."

Idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin raya kasa, Misereor na samun goyoyn bayan coci-coci a wasu sassa na Najeriya. Sai dai kuma tana daga cikin runkunin kungiyoyin da za a iya kai wa harin ta'addanci a kowane lokaci,kamar yadda ya faru da takwarorinta a baya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin