1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen mata a siyasar Najeriya

Binta Aliyu Zurmi YB
January 21, 2019

Matan da ke siyasa in ma dai wadanda aka zabe su ko wadanda a ka nadasu na fuskantar matsaloli inda wasu cikin al'umma ke masu kallon marasa mutunci, bayan kuwa suma suna da gudumawar bayarwa.

https://p.dw.com/p/3BvXp
Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
Hoto: Reuters/Sotunde

A lokuta da dama mata 'yan siyasa musammamn ma Musulmai na ganin ana amfani da addini ne wajen dankwafar da su daga shiga siyasa. Munira Tanimu Sulaiman wacce ta nemi tsayawa takara amma tun daga matakin zaben fidda gwani na jam'iya aka cire ta, a cewar ta anyi haka ne don kasancewar ta mace.

Hon. Maryam Garba Begel 'yar majalisa mai wakiltar mazabar Das a majalisar Jihar Bauchi na ganin wannan abu ba yau aka fara ba amma mata su sa hannu su toshe kunnuwansu su yi abin da ya kamata.

Nigeria Taraba Staat Frauen
Matan dai ana neman barinsu a layin zabe kawaiHoto: Picture alliance/dpa/epa/G. Esiri

Comrade Bako Abdul Usman shugaba na kasa a kungiyar Campaign for Democracy na ganin mata ma na da rawan takawa a siyasance. 'Yar siyasa Eunice Shehu kuwa da ke jihar Kaduna na ganin irin kallon da ake wa mata na sa wasu da ke da sha'awar ba da tasu gudumawar su ki fitowa. Amma ta ce kar su ji tsoro su fito.

Tabbas a kasashen duniya mata sun taka muhimiyar rawa a siyasa, Umar Muhammad Rigasa bai yarda da cewa matan banza ne kadai ke siyasa ba, ya ce a cikin kowane al'umma a kan sami nagari da kuma akasin haka, amma yin jama'u bai kamata ba.

Daga karshe Amina Mohammed shugabar kungiyar Haske Women and Youth Association of Nigeria na mai cewa mutunci dai riga ne idan ka kare kanka kowa ma zai kare ka.