KALUBALEN DAKE GABAN KUNGIYYAR EU | Siyasa | DW | 12.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KALUBALEN DAKE GABAN KUNGIYYAR EU

A yayin da shirye shirye a kungiyyar tarayyar turai suka yi nisa na shirin karbar sabbin mambobi a cikin ta da aka shirya yi a ranar daya ga watan mayu na wan nan shekara da muke ciki,a dai dai lokacin ne kuwa hukumar zartarwa ta Eu n ke tunanin yadda al,amarin ci gaban ta zai kasance bayan tabbatar da wan nan mataki data sako a gaba. A cewar kungiyoyi da dama masu zaman kansu a nan nahiyar Turai,Kungiyyar ta tarayyar turai zata samu ci gaba bayan karbar sabbin mambobin to amma kuma zata dingha cin karo akai akai da kalubae masu yawan gaske. Hujjar da kuwa wadan nan kungiyoyi masu zaman kann nasu suka bayar sun hada da cewa,da yawa daga cikin sabbin mambobin a baya sun dade suna karbar tallafi daga kungiyyar ta Eu.Bugu da kari a cewar kungiyoyin tattalin arzikin sabbin mambobin ba zai dace da tsarin yadda kungiyyar ta Eu ke gudanar da Al,amurranta na yau da kullum ba. A kuwa daya hannun bisa wan nan hujja da wadan nan kungiyoyi suka bayar tuni kungiyyar ta Eu tare da hadin gwiwar sabbin mambobin kasashen suka dukufa kain da nain wajen shirya tarurruka na karawa juna sani dangane da abubuwan da suka shafi kungiyyar da kuma ire iren aiyukan da take gudanarwa. A daya hannun kuma kungiyoyin sunyi ammanna da cewa sauran takwarorin su na sabbin mambobin kasashen nada kyakkyawar gudun mawa da zasu bayar wajen ci gaban mutanen kasashen nasu. Kungiyoyin sun kara da cewa takwarorin nasu ka kuma iya mayar da hankali wajen matsawa gwamnatocin nasu yakar fatara da kuma dangogin ta a cikin kasashen don ganin cewa kwalliya ta biya kudin sabulu wajen dai dai ta sahu da tsoffin mambobi kasashen na Eu. A kuwa ta bakin babban darakta mai kula da aiyukan ci gaba na kasar Ireland mai suna David Donoghue, babban abin da kungiyyar ta Eu tasa a gaba yanzu haka shine taga cewa duk sabbin mambobin kasashen sun samu taimakon daya dace don dai dai ta sahu da sauran tsoffin kasashe mambobi na kungiyyar,bisa hasashen cewa yin hakan ne kawai zai taimaka wajen bunkasa da kuma dorewar kungiyyar a nan gaba. Shi kuwa Franz Kaps daya daga cikin mutanen dake bawa bankin duniya shawara,cewa yayi bai kamata kungiyyar ta Eu ta dinga yin garaje ba wajen lalle sai sabbin kasashe mambobin sun dai dai ta da tsoffin ba,a maimakon hakan Franz yaci gaba da cewa kamatza yayi kwarya tabi kwarya har zuwa lokacin da sabbin mambobin kasashen zasu gane kabli da kuma ba,adi na kungiyyar ta Eu. Yin hakan a cewar Mr Franz sabbin kasashen zasu fi mayar da hankali wajen bada tasu gudummawar ta kudi ga hukumar dake kula da bayar da tallafin raya kasa ta kungiyyar ta Eu. A kuwa ta bakin kakakin hukumar zartarwa ta kungiyyar ta Eu,Jean Charles,cewa yayi a yanzu haka mun gano cewa matakin ci gaba da muka dauka a kungiyyar ba zai tasba canjawa a rana daya ba,sai dai sannu a hankali a don haka kungiyyar ta Eu zata tabbatar da cewa kasaashen yankin nahiyar Africa da karibiyan da kuma Facific basu jigata ba dangane da matakin fadada kungiyyar ta Eu. Sabbin dai kasashen da kungiyyar ta Eu zata karba a watan na mayu sun hadar da Estonia da Lithuania da Malta da Poland da Slovakia da slovenia da Cyprus da kuma kasar Czech.