Kalubalen da sana′ar kiwo ke fuskanta a Nijar | Zamantakewa | DW | 29.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kalubalen da sana'ar kiwo ke fuskanta a Nijar

Makjiyaya a Nijar sun bukaci hukumomi su shawo kan abubuwan da ke janyo musu cikas ga sana'arsu .

A dai dai lokacin da makiyaya a Jamhuriyar Nijar ke kokowa da matsalar rashin samun tallafi kamar irin na sauran al'ummar kasa, duk kuma da irin barazanar sace sacen dabbobin da suke fuskanta a cikin karkaru daban daban na kasar, Kungiyar makiyayan arewacin yankin Damagaram mai suna Co-operatives des Eleveurs Tende Belbeje Tarka ta gudanar da bikin sallar makiyayan dake bakin iyakokin jahohin Maradi, da Damagaram da kuma Agadez a arewa maso yammacin Tanout dake iyaka da Agadez.

Wanan Sallah dai ta wakana ne a ranaku biyu na karshen makon da ya gabata, inda kuma aka samu halartar dimbin makiyaya na ciki da wajen yankin Dmgaram, tare da kuma wakilan gwamnati da na 'yan majalisar dokoki. To sai dai batun matsalar sace-sacen dabbobi da aika-aikar da 'yan gadausa ke aikatawa a babban dajin Tende da kuma barazanar mamayar filayen kiwo daga masu gonaki su ne suka fi daukar hankali a ajandar taron. Agaly Haruna, shugaban shirya wannan taro yayi matashiya akan matsalolin.

Niger Tende Festival in Zinder

Mahalarta bukin Tende na makiyaya a Zinder, Nijar

Matsalolin da ke addabar makiyaya a Nijar

A yanzu dai daga masu dabbobin i zuwa makiyayan, da ma sarakunan yankin kuma a sahun gaba sarkin Tarka, duk sun koka da wadannan matsaloli kamar yadda malam Dilu ke cewa.

Ganin cewar dai daga mashawartan shugaban kasa Isuhu Mahamadu da kuma 'yan majalisar dokoki duk sun halarci taron na Tende, na ji ta bakin Alhaji Bukari Sani Zilly dan majalisar dokoki daga mazabar ta Tende.

Niger Tende Festival in Zinder

Wasu daga cikin matasan Fulani yayin bukin Tende a Zinder, Nijar

Kabilu biyu ne dai na makiyayan yankin suka halarci wannan biki na Abzinawa da kuma Fulani. To sai dai ba a sani ba ko koken makiyayan zai samu karbuwa cikin gaggawa kamar yadda suka bukata daga gwamnati.

Mawallafi : Larwana Malam Hami
Edita : Saleh Umar Saleh