Kalubale kan batun ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 14.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kalubale kan batun 'yan gudun hijira

Hukumar Tarayyar Turai ta zargi kasashe mambobin kungiyar EU da gaza cika alkawuran da suka dauka kan batun shawo kan matsalar kwararar 'yan gudun hijira a Turai.

Kalubalen 'yan gudun hijira a Turai

Kalubalen 'yan gudun hijira a Turai

Mataimakin shugaban hukumar Tarayyar ta Turai Frans Timmermans ne ya yi wannan zargin tare kuma ya bukatar shugabannin kasashen na EU da su shawo kan wannan matsalar a taronsu da za su yi cikin wannan mako. Kungiyar Tarayyar Turai dai na fuskantar gagarumin kalubale na kwararowar 'yan gudun hijira da ke tserewa kasashen da ke fama da yaki irin su Siriya inda suke zuwa Turai domin neman mafaka. A cewar kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ya zuwa Talata 13 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, akallah 'yan gudun hijira da ke neman mafaka sama da 593,000 suka shiga Turai ta Tekun Bahar Rum, wanda rabon da aga yawan 'yan gudun hijira irin haka tun lokacin yakin duniya na biyu. Batun 'yan gudun hijirar dai na kara zafafa ban-bancin ra'ayi a tsakanin kasashe 'ya'yan kungiyar ta EU.