Kalubale da ke gaban sabon shugaban kasar Faransa | BATUTUWA | DW | 08.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kalubale da ke gaban sabon shugaban kasar Faransa

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin zuba jari na makudan kudade domin fuskantar kalubalen da kasar ke ciki. Sai dai zaben 'yan majalisa na wata Juni mai zuwa zai zame masa kadangaren bakin tulu.

Frankreich Hollande und Macron beim Gedenken in Paris (Getty Images/AFP/S. De Sakutin)

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da Shugaba mai barin gado Fransoi Hollande.

Sabon Shugaba Emmanuel Macron dan shekaru 39 da haihuwa zai fuskanci kalubale ta fannoni da dama da zaran ya dauki madafun iko. Claire Dheret masaniya da ke cibiyar kula da manufofin siyasa na Turai ta ce zaben na Faransa ya sake bude wata taga ga Tarayyar Turai bisa samar da wasu manufofi wadanda za su gina kan wannan nasara:

Faransawa na jiran sauyi daga Macron

"Duk da 'yan Faransa sun zuba ido, suna cike da tsoro game da Tarayyar Turai bisa manufofin da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum, domin haka ina tunanin daya daga muhimman kalubalen shi ne, gano hanyar tattaunawa game da shirin Tarayyar Turai, kan manufofin kyautata rayuwa, kuma ina tutanin haka ke zama jan aiki da ke gaban Tarayyar Turai cikin shekaru masu zuwa."

Masaniyar Claire Dheret ta kara da cewa sabon shugaban na Faransa, tilas ya mayar da hankali bisa dangantaka ta hanyoyin aiwatarwa maimakon cece-kucen siyasa. Shi kansa Emmanuel Macron zababben shugaban na Faransa da zai dauki madafun iko ranar Lahadi mai zuwa ya nuna fahimta game da abin da zai fuskanta:

"A shekaru biyar masu zuwa, aikin da ke gaba na shi ne kawar da tsoro, da sake samar da fata na gari, da tababatar da abin da Faransa za ta iya game da komai. Aiki na shi ne tattara mata da maza wadanda suke shirye kan fuskantar gagarumin kalubalen da ke jiran mu, domin aiwatarwa.

Babban buri daga Sabon shugaban Faransa

Sai dai a cewar Farfesa Dominique Reynie masanin harkokin siyasa kana shugaban wata cibiyar kula da harkokin siyasa a Faransa da ake kira Fondapol, yana ganin nan gaba kadan kowa zai kara fahimtar kalubalen, bayan gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a watan gobe na Yuni.

Sabon Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya samu kashi 65 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda abokiyar adawarsa Marine Le Pen mai ra'ayin kyamar baki ta samu kashi 35 cikin 100 na kuri'un. Babban abin jira a gani, shi ne na kamun ludayin sabon shugaban idan ya dauki madafun ikon Faransa, daya daga cikin manyan kasashe masu karfin fada a ji a duniya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin