Tun bayan da aka kammala zaben shugaban kasa a Najeriya da bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe hankula sun karkata kan zaben gwamnoni da wasu jihohi ake da siyasa mai zafi a cikinsu.
An dai ga yadda siyasa ta dauki zafi a jihar Kano tsakanin 'yan takarar gwamnan jihar Kano gwamna mai ci Abdullahi Ganduje da Abba Kabir Yusuf. Haka nan jihar Kaduna inda Malam Nasir El-Rufa'i ke neman tazarce. A yankin kudanci kuwa fadace-fadace sun bayyana tun a zaben shugaban kasa.