1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kafa rundunar 'yan sandan jihohi

February 15, 2024

Bayan share tsawon lokaci ana kai-kawo, Tarayyar Najeriya ta amince da kafa rundunar 'yan sandan jihohi da nufin tunkarar matsalar rashin tsaron cikin kasar da ke sauya salo.

https://p.dw.com/p/4cRtF
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Taro | Gwamnoni | Matsaloli | 'Yan Sanda | Jihohi
Taro kan matsalolin kasa tsakanin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da gwamnoniHoto: Ubale Musa/DW

Wani taro a tsakanin shugaban kasar da gwamnonin jihohi ne dai, ke neman kai karshen doguwar takkadamar Najeriya kan batun tsaron. Bayan shafe tsawon kusan sa'o'i uku dai, an manta da bambancin da ke tsakani Kudu da Arewa da ma batun siyasa ta kasar mai zafi wajen amincewa da kafa rundunar 'yan sandan ta jihohin. Ana dai fama da satar al'umma cikin kasar, bayan alamu na gazawa a bangaren 'yan sandan tarayyar. Akwai dai zargin 'yan sandan tarayyar da karkata zuwa ga Abujar maimakon jihohi na kasar, wajen neman mafitar rikicin rashin tsaron da ke tashi da lafawa. To sai dai kuma daga dukkan alamu sabuwar dabarar ta burge su kansu ma su takama da adawar Najeriyar, a fadar Mani Malam Mummini Masamar Mudi da ke zaman mataimakin gwamnan Zamfara.

Najeriya | Maatsala | Rashin Tsaro | Jihohi | 'Yan Sanda
Ko samar da rundunar 'yan sandan jihohi zai magance matsalar tsaron Najeriya?Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Ko ma ya zuwa ina kokari na korar rabuwar ke iya kai wa a kokari na tunkarar rashin tsaron, shi kansa kokarin samar da abincin dai na kallon tunkarar masu boye abincin da ke a sassan Najeriyar dabam-dabam. Najeriyar dai ta ce, za ta yi amfani da jami'an tsaro wajen bankado da kwace abincin da ke a boye a shaguna dabam-dabam cikin kasar. Aminu Abdusallam dai na zaman mataimakin gwamnan Kano, jihar kuma da tuni ta dauki karatun kwace abincin da ke a shaguna, kuma ya ce ana tunanin dorawa zuwa dala a kokarin neman mafitar rikicin cikin kasar na abinci. Abujar dai ta ce ba ta nshirin shigo da abinci zuwa cikin kasar ko mai runtsi da nufin kaucewa mai da hannu na agogo zuwa baya, cikin batu na ci da kai da ke zaman babban kwazo.