1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna : Shirin rarraba magunguna ta jiragen sama

Abdourahamane Hassane
June 3, 2022

Wani kamfani mallakar Amirka da ke kai kayayyakin kiwon lafiya da magunguna ta hanyar jirage marasa matuka ya sanar da cewar ya fara tashin jiragensa a Jihar Kaduna.

https://p.dw.com/p/4CH3I
NO FLASH Drohne vom Typ MQ-1 Predator
Hoto: picture alliance/dpa

Miliyoyin mutane ne dai a yankin arewacin Najeriya ke da karancin hanyoyin samun kulawa ta kiwon lafiya musamman saboda kasancewar kungiyoyin masu jihadi. A cewar kamfanin mai sunan Zipline mai kyara jirage marasa matuka, jiragen za su isar da kayayyakin kiwon lafiya  da magunguna sama da 200 a fadin Jihar Kadunan,a wani mataki na gwaji kafin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta amince da aiwatar da shirin a hukumance.