Jonathan zai yi takara a 2015 | Siyasa | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jonathan zai yi takara a 2015

Batun tsayawa takarar Jonathan a shekara ta 2015 ya kawo karshen jiran da aka dade ana yi na sanin matsayin shugaban wanda ke da tasirin gaske a fagen siyasar kasar.

A karon farko mutumin da ake ganin na da ikon fada a ji a a kololuwar jamiyyar PDP Chief Tony Anenih, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na jamiyyar PDP ya bayyana cewa shugaba Jonathan zai sake neman takarar shugabancin kasar a 2015 a yanayin da ke nuna kawo karshen dogon jiran da aka dade ana yi a kan wannan batu da ke da tasiri a zaben 2015 da ke fsukantar Najeriyar.

Sanin matsayi da ma kusancin Chief Tony Anenih ga shugaban na Najeriya ya sanya jinjinan kalaman nasa da ke bada tabbacin cewa lallai shugaban Jonathan din zai yi takara a zaben na 2015, da ake zura idanun sanin alkibilarsa.

Shugaban Najeriyar dai ya dade yana kaucewa batun ko zai tsaya takara a zaben na 2015 ko a'a, inda yakan ce lokaci bai yi ba da zai ambata haka, abin da ya sanya ci gaba da wasan boyo ga ‘yan Najeriya da dama da ke jiran sanin inda ya dosa da zai iya nuna akalar siyasar kasar. To ko yayya yayan jamiyyar suka ji da kallaman na Chief Tony Anenih? Alhaji Isah Tafida Mapindi jigo ne a jamiyyar ta PDP kuma ma dan kwamitin zartsawa na jamiyyar.

‘'A tafiyar PDP jam'iyya ce wacce take da ladabi da tsari babu wani a cikin PDP wanda zai hana shugaba ya tsaya takara sai in tsarin mulki ya hana shi, kuma tsarin mulkin ma ba zai hana shi ba, kuma wannan Magana ce da aka yi a wurin mutanen day a dace a yi. A jam'iyyance muna tsamanin Jonathan zai tsaya takara da mataimakinsa Architect Namadi Sambo domin tafiyasru zata yi tsari don tafiya ce wacce jamiyya ta amince''.

Jinkirin rashin sanin wanene zai tsaya takara a manyan jamiyyun Najeriyar biyu na PDP da ke mulki da APC ta ‘yan adawa ya sanya shiga yanayin cirko-cirko a siyasar kasar duk da cewa sauran watani shida a gudanar da zaben da aka ci ma shi buri fiye da zabubbuka da suka gabata a kasar, musamman saboda kalubale na rashin tsaro da ke adabar Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin