1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joko Widodo ya gayaci Putin a taron G20

Abdourahamane Hassane
June 29, 2022

Shugaban Kasar Indonesiya Joko Widodo, wanda ke jagorantar kungiyar G20, ya isa Kyiv babban birnin kasar Ukraine a matsayin wanda ya nada kansa mai shiga tsakani na neman zaman lafiya tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4DQs9
Ukraine Krieg, Joko Widodo zu Besuch in Kiew
Hoto: Agus Suparto/Indonesian Presidential Palace/AP Photo/picture alliance

Daga kiev shugaban na Indonesiya zai tafi Rasha don ganawa da takwaransa Vladimir Putin,domin gabatar da bukatar kawo karshen yakin don kaucewa matsalar karancin abinci a duniya.I  Indonesiya za ta karbi bakuncin taron kasashe masu arzikin masana'antu G20 a Tsibirin Bali a watan Nuwamba da ke tafe.