John Kerry na shirin zuwa Najeriya kan Boko Haram | Labarai | DW | 23.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

John Kerry na shirin zuwa Najeriya kan Boko Haram

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya sanar da aniyarsa ta zuwa Najeriya nan da 'yan kwanaki kalilan, kasar da ke fama da matsalar kungiyar Boko Haram.

Kerry ya sanar da aniyar ce a yau Jumma'a, cikin wani jawabi da ya yi kan harkokin ta'addanci a babban taron kasashen duniya kan tattalin arziki da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland. John Kerry ya yi jan hankali na ganin cewa kada a karkata akalar ya zuwa kyamar Yahudawa ko kuma kyamar mabiya addinin Islama, a yakin da ake yi da 'yan kungiyar IS, da Al-Qaida ko kuma Boko Haram.

Kasar ta Najeriya dai na cikin shirye-shiryen zaben shugaban kasa da 'yan majalisun Tarayya da za su gudana a ranar 14 ga wata Febrairu mai zuwa, inda a wannan Jumma'ar hukumar zaben kasar ta tabbatar cewa, ba za a daga zabe ba kamar yadda wasu ke neman ayi

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman