1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: JNIM na neman hadin kai don kifar da gwamnatin soji

May 1, 2026

Kungiyar JNIM ta bukaci hadin kan 'yan Mali domin kawar da sojoji daga kan madafun iko, bayan ta killace Bamako babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/5D7K0
Mali Kidal 2026 | Tuareg-Rebellen der FLA-Koalition versammeln sich am Kreisverkehr
Hoto: AFP

Kungiyar jihadi ta JNIM mai alaka da Al-Qaida ta yi kira ga dukkan 'yan Mali, kama daga jam'iyyun siyasa zuwa sojoji da malaman addini da shugabannin gargajiya da su hada kai da ita domin kawo karshen mulkin soji da kuma shinfida mulkin rikon kwarya cikin lumana, wanda a cewarta zai bai wa shari’ar Musulunci muhimmanci.

Ko harin Mali zai zama ishara ga Nijar?

A daidai wannan lokaci gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da cewa rundunar hadin gwiwa da kasashen AES suka kafa ta kai farmaki a arewacin Mali kan mayakan jihadi, jim kadan bayan hare-haren da suka kai wasu sassan Malin a karshen makon da ya shige.

Gwamantin Nijar ta yaba da luguden wutar ta sama kan biranen Gao da Meneka da kuma Kidal da rundunar hadin gwiwa ta kasashen uku na yankin Sahel ta yi a matsayin martanin gaggawa.

Har ila yau a ranar Alhamis an gudanar da zana'izar tare da girmama tsohon ministan tsaron Mali marigayi Janar Sadio Camara, wanda harin ranar 25 ga watan Afrilu ya ritsa da shi da na iyalansa.