Jirgin sama na Rasha ya bace da fasinjoji 91 | Labarai | DW | 25.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama na Rasha ya bace da fasinjoji 91

Wani jirgin sama na sojan kasar Rasha dauke da mutane 91 ya yi batan dabo jim kadan bayan da ya taso daga birnin Adler na Kudancin kasar. 

Ministan tsaron kasar ta Rasha wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce jirgin na dauke da fasinjoji 83 akasarinsu manyan sojojin kasar ta Rasha da kuma ma'aikatan jirgin guda takwas da 'yan jarida guda tara a lokacin da ya bace daga allon na'urarar kula da tafiyar jirgin sama.  

Jirgin ya taso ne da misalin karfe biyar da mintoci 40 wato biyu da minti 40 agogon GMT daga birnin Adler zuwa filin jiragen sama na sojan Rasha na Hmeimim da ke kusa da birnin Lattaquie na Arewa maso Yammacin kasar Siriya inda mutanen za su halarci bikin sallar kirsimeti da aka shirya a barikin sojojin ta Hmeimin.Sai dai wasu rahotanni da ke shigowa yanzu na cewa ministan tsaron kasar ta Rasha ya ce an gano wasu sassan jirgin a cikin ruwan Bahar Asuwad.