Jiran sakamakon zaben Najeriya | Labarai | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiran sakamakon zaben Najeriya

Ana sa ran fara samun sakamakon farko na zaben shugaban Najeriya da aka gudanar karshen mako a fadin kasar.

A wannan Litinin ake sa ran fara bayyana sakamakon farko na zaben shugaban kasa a Najeriya a hukumance, kamar yadda hukumar zaben kasar ta nunar. Ana fafatawa mai zafi tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP mai mulki da kuma madugun 'yan adawa Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran kwantar da hankali yayin da ake zaman jiran sakamakon zaben na shugaban kasa. A wasu sassa na kasar an tsawaita zaben na ranar Asabar zuwa ranar Lahadi, saboda wasu matsaloli da aka samu. Wannan zaben ke zama kalubale mafi girma da jam'iyyar PDP ta fuskanta tun bayan komawar Najeriya bisa tafarkin demokaradiyya a shekarar 1999.