Jiragen yakin kasar Kameru sun yi ruwan wuta kan ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 29.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen yakin kasar Kameru sun yi ruwan wuta kan 'yan Boko Haram

Sojojin Kameru na ci gaba da fatattakan tsagerun Boko Haram

Gwamnatin kasar Kameru ta bayyana cewa jiragen yakin kasar sun yi ruwan bama-bamai kan tawogar 'yan Boko Haram a yankin arewa mai nisa na kasar.

Shugaban Kasar Paul Biya ya ba da umurnin kai farmakin sama kan 'yan Boko Haram, kuma wasu daga cikin da suka tsira sun tsere suka sake komawa Najeriya, kamar yadda ministan sadarwa na kasar ta Kameru, Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar a cikin wata sanarwa.

Rahotanni sun ce sojojin kasar ta Kameru sun hallaka tsagerun Boko Haram fiye da 40 lokacin hare-hare.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar