1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkiri wajen kafa rundunar G5 Sahel

Abdoulaye Mamane Amadou
September 14, 2017

Hukumomin Mali da na Nijar sun nuna damuwa game da dari-darin da wasu manyan kasashen duniya ke nunawa wajen bayar da tallafin kudaden girka rundunar da zata yaki 'yan ta'adda a tsakanin kasashen biyar na G5 Sahel

https://p.dw.com/p/2jzL7
Gipfeltreffen in Bamako Mali
Hoto: Reuters/L. Gnago

Shugaba Ibrahim Boubakar Keita kenan na kasar Mali a ya yin ganawa da manema labaru a Yamai da yammacin Laraba sakamakon wata ziyarar aiki ta wuni daya da shugaban ya kai a Nijar biyo bayan rangadinsa a tsakanin kasashen G5 Sahel da zummar cimma matsaya daya da kasashen manbobin kungiyar, don tunkarar manyan kasashen duniya a babban taron Majalisar Dunkin Duniya da a ke shirin gudanarwa.

A gaban manema labaru shugaban ya ce kungiyar da rundunarta mai askarawa a kalla dubu biyar ta riga ta share fagen nuna cewar za ta iya, saboda hakan dole ne kasashen duniya su yarda da wannan matsayi.

 Ya ce "yanzu hakan dai ina mai tsammanin cewar G5 Sahel na cigaba da nuna matsayinta da ma iyawarta a bainar kasashe kana kuma yana da kyau a cikin tafiya idan har bukata ta taso da mu hadu don tattaunawa musamman ma a gabanin wasu manyan taruruka na duniya da niyar cimma matsaya daya da zamu iya dogaro da ita madaidaiciya musamman ma a gabanin taron koli na majalisar dunkin duniya; na hadu da shugaban kasar Murtaniya bayan ganawa da na kasar Tchadi a yau gani a Nijar zan kuma wuce zuwa Burkina Faso don tattaunawa domin samun murya daya hadaddiya da bata da wata tababa".

Gipfeltreffen in Bamako Mali
Hoto: Reuters/C. Archambault

Ya zuwa yanzu dai kasashen na G5 Sahel na bukatar makudan kudade ne fiye da Euro miliyan 423, inda kawo yanzu basu wuce 1/4 ba kawai na kudaden ba da suka samu ba a matsayin tallafi duba da raunin da kasashen suke da shin a fannin tattalin arziki da ke hana su daukar kansu da kansa.

Gwamnatocin kasashen sun bayar da nasu gudunmowa

A cewar Ministan harkokin wajen Nijar Malam Ibrahim Yacouba gwamnatocin kasashen sun riga sun yi iyakacin nasu kokari:

 

Ya ce "mun gwada mun yi niyya mun bada soja da hadin kai. Kenan abin da ya rage shi ne duniya ta bada hadin kai, kuma bamu nan ga gane yanda suke jan kafa alhali kuwa su na da soka sun san yanda kasashen mu suke ciki suna da kayan aiki a kasashenmu Kenan mu tsamaninmu idan harm un ce muna bukatar taimako to kamata ya yi su kama muna, ina ganin kamar ba su taba yin shi taimakon e don shi ne suke dari dari to amma mu da muna da karfi da gaskiya ba zamu bidi taimakonsu ba.

Kasashen biyar na G5 Sahel a cewar gwamnatin Jamhuriyar Nijer za su ci gaba da jajircewa face sai sun cimma wanna guri na kawo karshen duk wasu aiyukan ta'addanci da ke addabar yankin sahel saboda hakan Nijar ta ce tana fatan bayanan da manbobin kungiyar za su gabatar a gaba zai kai ga gamsar da daukacin kasashen dunniya.

Yace "kokuwar tsaron kasa kokuwa ce da ba yanda za'a yi sai an yita saboda ba za mu bar kasashenmu 'yan ta'adda su halaka su ba. Sojan kasashen duniya dubu 13 da aka aiko a MUNUSMA wanda shekara duk dalar Amirka Biliyan daya ake kashewa, kuma har yanzu basu tabuka komai ba kuma an kashe masu fiye da mutun 140. To mu muna cewar a bamu kawai rabin wadannan kudaden ko ma kashi guda ya isa muyi aikin kuma mu ci nasara, saboda hakan kasashen da ke jan kafa basu da wannan iznin kuma ba zamu bari su huta ba".

Afrika Niger - Ursula von der Leyen und Flaurence Parly
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

 

Fara aikin rundunar G5 Sahel

A cikin watan gobe ne dai ake sa tsamanin rundunar zata fara aikinta gadan gadan inda za'a kasa ta har kashi uku da kuma zata hada hantunan kasashen biyar don tabbatar da tsaron kasashen da na duniya baki daya lamarin da a cewar shugaba Issoufou muddin akayi sake shimgen da suke rige da shin a yan ta'adda ya katse to baa bin mamaki ba ne yan ta'adda su fantsama zuwa Turai ko kasashen Amirka don haka dole ne kasashen su kamawa G5 maimakon zura masu ido kurum.

Idan har Rundunar tabkin Chadi ta samu nasarar karya lagon boko haram hakan na faruwa ne saboda tallafi mafi tsoka da Tarayyar Najeriya ke bayarwa to amma sai dai a nan banbancin shine a G5 Sahel babu wata kasa da ke iya zuba makudan kudin yaki da ta'addanci kamar tarayyar Najeriya Inji shugaba Issoufou da ya ke kammala jawabinsa.