1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigilar 'yan Nijar mazauna Afirka ta Tsakiya

January 6, 2014

Gwamnatin Nijar ta bi sahun sauran takwarorinta na wasu kasashen Afirka wajen kwaso 'yan asalin kasarta mazauna Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ke fama da rikici.

https://p.dw.com/p/1Am3H
Zentralafrikanische Republik Elend
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

'Yan asalin kasar ta Nijar sama da 1,000 ne yaki ya rutsa da su a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya wacce ta fada cikin rikicin kabilanci da addini, musamman a makonnin baya bayannan, inda a yanzu gwamnati ta basu mafaka a sansanin da ta kebe a filin sauka da tashin jiragen saman birnin Yamai.

Tun a ranar Jumma'a dai ne jirgin farko ya kwaso sama da mutane 150 kuma kawo yanzu jirgin ya yi sawu hudu inda ya kawo kusan mutane 700 daga cikin kimanin dubu na 'yan asalin kasar ta Nijar da aka yi rajistarsu a birnin Bangui. Jim kadan bayan isowarsu gida, wasunsu sun bayyana farin cikinsu dama halin da suka tsinci kansu a cikinsa a can kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Rafini, Ministerpräsident Niger
Fira ministan Nijar, Birji RafiniHoto: DW

Kyakkyawan tanadi ga 'yan gudun hijirar Nijar

Bakin dai sun samu kyakyawan tarba daga jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira reshen kasar Nijar, da kuma mambobin wani kwamiti na musamman da gwamnatin Nijar din ta kafa domin kula da tarbon 'yan Nijar da ke dawowa daga kasashen ketare a cikin irin wannan hali, kuma shugabar wannan hukuma Malama Sa'adatu Malam Barmo, ta yi tsokaci dangane da wannan aiki na tarbon bakin tana mai cewar gwamnatin Nijar ta tanadi dukkan abubuwan da suke bukata har lokacin da za su hadu da danginsu mazauna Nijar.

Sai dai duk da wadannan kiraye-kiraye na gwamnati, yanzu haka 'yan Nijar da dama ne su ka zabi ci gaba da kasancewa a halin yanzu a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Malam Idrissa Abubakar na daga cikin jerin wadannan mutane, kuma ta wayar tarho ya bayyan mana dalillansu na daukar wanann mataki, inda ya ce sun tsaya ne domin kare dukiyoyinsu, kuma suna fata ko da bayan rikicin ne, za su iya sayar da kayayyakinsu domin komawa gida Nijar.

Französische Truppen patrouillieren in Zentralafrikanischer Republik 8.12.13
Dakarun ketare a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: S.Kambou/AFP/GettyImages

A wannan Litinin ce (06.01.14) dai ne ake sa ran jirgi zai yi sawun karshe na jigilar yan Nijar din daga kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a yayin da gwamnatin ta soma shirye-shiryen isar da bakin zuwa garuruwansu na asali.

Mawallafi : Gazali Abdou Tasawa
Edita : Saleh Umar Saleh