Jawabin shiga 2013 na Merkel ga jamusawa | Labarai | DW | 01.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin shiga 2013 na Merkel ga jamusawa

Angela Merkel ta bayyana cewa har yanzu da sauran rina a kaba game da matsalar kudi da ta addabi Turai. Hakazalika ta tabo batun tsaro na ciki Jamus da na kasashen duniya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi amfani da jawabin shiga sabuwar shekara ta 2013 wajen yin kira ga 'yan kasarta da su zage dantse domin taimaka wa kasar samun ci gaba mai ma'ana. Cikin jawabin da ta yi ta kafar telebijin Merkel ta ce Jamus na bukatan yin aikin tukuru domin fuskantar matsalar tattalin arzikin da ke addabar kasashen Turai.

Merkel ta kuma yi gargadi game da dimbin kalubale da za a iya fiskanta a sabuwar shekara ta 2013, sabanin tabbacin ci gaba da ministan kudi Wolfgang Schaueble ya bayar a makon da ya gabata. Ya na mai cewa matsalar ta tattalin arziki ta zama a tarihi a Jamus da ke zama kasar da ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai.

A lokacin da ta tabo batun tsaro na cikin gida, Merkel ta mika godiya ga sojoji da jami'an 'yan sanda da ma dai ma'aikatan gwamnati saboda gudunmawar da su ka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Jamus da ma duniya baki daya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi