Tinubu ya janye wa ministoci 'yan sanda
December 10, 2025
Wajen wani taron majalisar zatarwar kasar ne dai, shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya ce duk wani ministan da ke bukatar kariyar jami'an tsaron, to ya nemi rundunar kare fararen hula. Jan idon shugaban dai, na nuna irin damuwar gwamnatin kasar kan ingantar harkar tsaro.
Gargadi mai karfi
Duk da shafe kusan tsawon makonni uku da janye jami'an 'yan sanda daga kare manya, har ya zuwa yanzu 'yan sandan ne ke kare ministoci na gwamnatin tarayyar. Shugaba Tinubun dai ya kalli cikin idonsu ya shaida musu cewar daga yanzu ba ya son ganin kowane dan sanda da sunan kare wani minista.
"Na kira babban sufeton 'yan sanda kuma ina fatan ministan 'yan sanda na nan, inhar kuna da matsala saboda yanayin aikinku to ku tuntubi babban sufeton 'yan sanda, shi kuma ya nemi amincewata. Kai kuma ministan cikin gida, ka hada kai da jami'an kare fararen hula domin maye gurbin 'yan sandan da ke aikin kare manya....." A cewar Shugaba Tinubu.
To sai dai kuma ko bayan umarnin, ShugabaTinubun ya gana da babban sufeton 'yan sandan kasar da ma mashawarci na tsaro da nufin tabbatar da aiwatar da sabon umarnin. Sabon matakin dai daga dukkan alamu ya sosa ran ministoci, inda da yawa suka fito cikin zauren taron rai a bace. Akwai dai tsoron gaza sauke nauyi a bangaren ministocin da ke da jan aikin shiga cikin al'umma ba tare da walwalar iya sauke nauyin ba.
Ko umurnin zai yi tasiri?
A baya dai bisa al'ada, a kan samu kimanin motocin 'yan sanda biyu da ke rakiyar ministocin. Abdulkadir Indabawa dai, tsohon kwamishinan 'yan sanda ne a kasar da kuma ya ce: "Da kamar wuya umarnin shugaban ya yi tasiri a kasar da 'yan sandan ke zama alamun iko".
Wata runduna ta musamman ta jami'an 'yan sandan na ta farautar 'yan sandan a ofisoshin ministocin, to sai dai kuma majiyoyi sun ce tuni suka cire kayan aikinsu, domin ci gaba da bayar da kariyar da ke da tasirin gaske.
Amma kuma a tunanin Dakta Yerima Lawal Ngama da ke zaman wani tsohon minista a gwamnatin ta Abuja, ministocin ba sa bukatar kariyar 'yan sanda kafin su iya gudanar da aikinsu. Tarayyar Najeriyar na fatan kara yawan 'yan sandan, ka iya taimakawa rundunar da ke da jan aikin kare kasar cikin rashi isassun jami'ai da ma kayan aiki.