1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar Musa zai maye gurbin Badaru a ma'aikatar tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
December 2, 2025

Kwana daya bayan murabus da Mohammed Badaru Abubakar ya yi daga mukamin ministan tsaron Najeriya, Shugaba Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon ministan tsaro.

https://p.dw.com/p/54eAV
Janar Christopher Musa sabon ministan tsaron Najeriya
Janar Christopher Musa sabon ministan tsaron NajeriyaHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Shugaban Bola Ahmad Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon ministan tsaro na kasa. A cikin wata wasikar da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Janar Musa zai maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus  bisa dalilai na rashin lafiya.

Janar Musa gogaggen soja a ma'aikatar tsaron Najeriya

Janar Musa, wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamban 2025, fitaccen soja ne da ya jagoranci rundunar tsaron Najeriya a tsakanin shekarar 2023 zuwa Oktoba 2025. Ya kuma taba lashe lambar yabo ta Colin Powell Award for Soldiering a shekara ta 2012.

Ta'asar 'yan bindiga na satar dalibai a Najeriya

An haifi Janar Musa a jihar Sokoto a 1967, kuma ya yi makarantar firamare da sakandare a jihar, kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986, sannan ya shiga ma'aikatar horon aikin soja ta Nigerian Defence Academy, inda ya samu digirin farko a 1991.

Shugaba Tinubu na da kyakyawan fata ga Janar Christopher

Hafsoshin kasashen waje a yayin taron da suka gudanar a Abuja
Hafsoshin kasashen waje a yayin taron da suka gudanar a AbujaHoto: KOLA SULAIMON/AFP

A 2019, Janar Musa ya jagoranci sashe na uku na runduna ta musamman ta "Operation Lafiya Dole", tare da jagorantar sashe na uku na rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ke yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

A cikin wasikarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa cewa Janar Musa zai kara inganta tsaron Najeriya tare da jagorantar ma’aikatar tsaron kasar kamar yadda ya kamata.