Janye tallafin man fetir ya jawo cece-kuce a Najeriya | Siyasa | DW | 12.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Janye tallafin man fetir ya jawo cece-kuce a Najeriya

Kungiyar kwadagon Najeriya ta ce ba za ta amince da karin farashin man fetir din da gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanar ba kuma za ta kalubalanci matakin.

Karin kudin man fetur na shirin jefa talaka cikin halin tasku a Najeriya

Karin kudin man fetur na shirin jefa talaka cikin halin tasku a Najeriya

Gwamnatin Najeriyar karkashin jagorancin Muhammadu Buhari mai taken canji ta yi wa batun tallafin man fetir din Najeriyar da ke cike da takaddama kifa daya kwala, inda ta sanar da janye tallafin tare da yin karin farashin daga Naira 86.50 zuwa Naira 145, abin da ya nina kari na sama da kashi 80 cikin 100.

Gwamnatin na mai dagewa kan cewar wannan zai sanya wadatuwar man fetir din da ‘yan Najeriya suka kwashe watanni na fama da karancinsa. To sai dai kungiyar kwadagon kasar da ta dade da adawa da duk wani yunkuri na janye talafi, ta ce ba fa za ta sabu ba kamar yadda Comrade Nuhu Toro mai taimaka wa shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ya bayyana.

Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010

Gangamin 'yan kwadago a Najeriya

Karin farashin mai dai a Najeriya a kowane lokaci kan fuskanci martani na bai daya daga al'ummar kasar, musamman saboda yadda lamarin kan shafi rayuwar talaka, amma a wannan karon da alamun ra'ayoyi na shan bam-bam tsakanin ‘yan Najeriyar kamar yadda wasu suka bayyana a Abuja.

To amma ga Mustapha Fanandas daya daga cikin matsan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na mai bayyana adawarsu da wannan kari. A ranar Jumma'a ce dai kungiyar kwadago a Najeriyar ke shirin taro wanda talakawan kasar ke jira su ga yadda za ta kaya.

Sauti da bidiyo akan labarin