Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa kan sakewa Najeriyar fasali, a dai dai lokacin da ake neman shawo kan masu kiran aware.
Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya ta bukaci gwamnati da ta dauki mataki a kan ci gaba da dauki dai dai da ake wa Fulani makiyaya a kudancin kasar.
A daidai lokacin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta rasa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, jam'iyyar ta sanar da yin watsi da tsarin karba-karba da ke a cikin tsarinta na zaben shugaban kasa.
Zaben fidda gwani tsakanin 'yan takara ya bullo da sabon salo a siyasar Najeriya, inda wasu ‘yan takara duk da ficen da suka yi a yankunana da dama, sun kasa samun ko da kuri’a daya.
Mayakan Boko Haram sun halaka masunta da dama a kwatar Kaulaha da ke tsibirin tafkin Chadi a kan iyakokin tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya haddasa halin firgici da tashin hankali.