Jan Egeland ya maida martani ga haramcin da gwamnatin Sudan tayi masa na ziyartar Darfur | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jan Egeland ya maida martani ga haramcin da gwamnatin Sudan tayi masa na ziyartar Darfur

Mataimakin sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da bada agaji, Jan Egelend, ya maida martani, da haramcin da hukumomin Sudan su ka yi masa, na kai ziyarar gani da ido a yankin Darfur.

Idan ba a manta ba ranar, litinin da ta wuce, gwamnatin Khartum ,ta ƙi baiwa Sakataren, izinin gudanar da rangadi a wanan yanki , da ke fama da yaƙe yaƙe.

A cikin martanin da ya maida, Jan Egeland, ya bayyana matukar takaici ,ga wannan mataki da hukumomin Sudan su ka ɗauka.