Jamus: Ebola ta dauki hanyar zama tarihi | Labarai | DW | 05.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Ebola ta dauki hanyar zama tarihi

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da tabbacin cewa ko adadin sabbin kamuwa da cutar ya ragu sosai.

Walter Lindner Ebola-Beauftragter der Bundesregierung mit Hermann Gröhe und Gerd Müller

Jami'ai a tawagar yaki da cutar Ebola daga Jamus

A kasashen yankin yammacin Afirkan da suka kamu da Ebola, alkaluma sun nuna cewa an yi nasara a dakile yaduwar cutar, kuma bisa irin bayanan da ta samu dangane da wannan batu, gwamnatin Jamus na kyautata zaton cewa daga nan zuwa tsakiyar wannan watan na Mayu za a iya kaiwa ga dakile cutar.

Manzon na musamman dangane da cutar ta Ebola, wanda kuma shi ne ke kula da aiyukan agajin da Jamus ta shirye dan yaki da Ebola, Walter Lindner ne ya bayyana hakan. Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da tabbacin cewa ko adadin sabbin kamuwa da cutar ya ragu sosai, kamar yadda shi kansa Lindner ya bayyana:

"A watan Janairun wannan shekarar, akalla mutane 400 ne aka gano dauke da cutar a karon farko, a kasashen Laberiyar, Saliyo da Guinea a hade, amma a 'yan makonnin da suka gabata akan samu mutane akalla 30, wani lokaci su kai haka, koma ba zasu ma kai haka ba".