1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: CDU ta cimma matsaya

April 20, 2021

Jam'iyar CDU mai mulki a Jamus da sanyin safiyar yau Talata ta sanar da sunan Armin Laschet a matsayin dan takararta a zabukan kasar masu zuwa.

https://p.dw.com/p/3sFvC
Deutschland Berlin | Armin Laschet CDU Kanzlerkandidat
Hoto: Marksu Schreiber/AFP/Getty Images

Armin Laschet da ke samun goyon bayan shugaba Angela Merkel, ya buge abokin hamayarsa Markus Soeder da kaso 77.5 cikin dari bayan wata kuri'ar raba gardama da jigajigan jam'iyar tasu ta CDU suka kada a daren jiya Litinin.

Tun dai a makon da ya gabata ne ake kai ruwa rana, dangane da wanda zai gaji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ma damar jam'iyar CDU din ta yi nasara a zaben kasar da za a gudanar nan da watan Satumbar wannan shekarar da muke ciki.