Jamian tsaron Pakistan sunce,an kashe kwararre a fannin makamai masu guba na Alqaeda | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamian tsaron Pakistan sunce,an kashe kwararre a fannin makamai masu guba na Alqaeda

Jamian tsaro a kasar Pakistan,sun baiyana kashe wani dan kungiyar Alqeada da Amurkan take nema ruwa a jallo kuma dan uwan na hannun daman Osama bin laden Ayman Azzawahiri,cikin harin makamai masu linzami da Amurka ta kai a makon daya gabata.

Mahukuntan kasar Pakistan sunce,akalla yan bindiga na kasashen ketare 4 ne aka kashe cikin wannan hari a garin Damadola dake kusa da bakin iyaka kasar da Afghanistan.

Wani jamin tsaro da ya nemi a boye sunansa yace, an kashe wani dan kasar Masar Midhat Mursi al Sayyidi,wanda kasar Amurka tace kwararre ne wajen kera bam bamai da sarrafa guba,wanda kuma ke da sansanin horasda yan taada a yankin Derunta dake kusa da birnin Jalalabad na kasar Afghanistan.

Inda aka ce ya horasda daruruwan mujahidai.