1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jami'an filin jirgin Heathrow na London za su yi yajin aiki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2024

Ma'aikatan su sama da 300, za su fara yajin aikin ne a ranar 29 ga watan, zuwa 2 ga watan Mayu mai kamawa

https://p.dw.com/p/4erIa
Hoto: Steve Parsons/empics/picture alliance

Daruruwan jami'an tsaron kula da iyaka na filin jirgin saman Heathrow da ke birnin London, za su fara yajin aiki a cikin wannan wata na Afirilu, sakamakon kokawa da suka yi kan halin da yanayin aikinsu ke ciki.

Karin bayani:An sake rufe filin jirgin sama na Gatwick

Ma'aikatan su sama da 300, za su fara yajin aikin ne a ranar 29 ga watan, zuwa 2 ga watan Mayu mai kamawa, in ji babbar sakatariyar kungiyar kwadagonsu Fran Heathcote.

Karin bayani:'Yan sandan Burtaniya sun cafke wanda ya gabza motarsa da kofar fadar masarautar kasar ta Buckingham

A shekarar 2022 da jami'an suka tsunduma irin wannan yajin aiki, gwamnatin Burtaniya ta sanya sojoji gudanar da aikin binciken fasfo din matafiya, a filin jirgin saman na Heathrow, wanda ke zama daya daga cikin manyan filayen jiragen sama da suka fi fice a duniya.