An sake rufe filin jirgin sama na Gatwick | Labarai | DW | 21.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake rufe filin jirgin sama na Gatwick

An sake rufe filin jirgin sama na Gatwick a London bayan da ake zargin an sake hango jirage marasa matuka suna shawagi a kusa da filin jirgin a yammacin wannan Juma'ar.

Hukumomin filin jirgin sama na Gatwick suna binciken rahotannin sake hangen jirage marasa matuka da ke shawagi kusa da filin jirgin.

A cikin wata sanarwa da hukumomin suka wallafa a shafin Twitter sun ce an sake rufe filin jirgin saman bisa matakai na tsaro.

Sake rufe filin jirgin sama na zuwa ne kwana daya bayan bude filin jirgin bayan rudanin da aka fuskanta na jirage marasa matuka da aka hango sun ratsa ta filin jirgin wanda ya sa aka soke tashi da saukar jirage tsawon kwanaki uku da suka wuce.

Yan sanda na cigaba da farautar wadanda suka sarrafa jiragen marasa matuka da suka ratsa filin jirgin, yayin da aka jibge sojoji domin tsaron filin jirgin saman na Gatwick da ke zama na biyu mafi girman hada hadar jama'a.

Mataimakin shugaban yan sanda na yankin Sussex Steve Barry ya yi bayani yana mai cewar:

"Yace akwai zakakuran mutanen mu da ke aiki, kuma aikin na tafiya yadda ya kamata. Akwai wasu bangarori da muke bincike da kuma wasu mutane da muke yiwa tambayoyi. Abin da za mu ce kawai shine muna bukatar jama'a su taimaka mana da bayanai game da halayyar wasu mutane da suke da shakku akan su da suka ga suna sarrafa jirage marasa matuka".

Tun daga ranar larabar da ta gabata an ga giftawar jiragen marasa matuka har sau 50.