1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jack ma ya baiwa Najeriya kayan yaki da corona

Binta Aliyu Zurmi
March 25, 2020

Najeriya ta karbi sakon agajin kayan yaki da cutar annobar Coronavirus daga attajirin biloniyan nan na kasar China Jack Ma mai kamfanin AliBaba.

https://p.dw.com/p/3a2Hn
Frankreich Paris | Jack Ma CEO von Alibaba
Hoto: Getty Images/AFP/P. Lopez

Jiirgi ya sauka dauke da kayayaki da suka hada da akwatunan gwajin cutar guda dubu ashirin da takunkumi guda dubu dari da rigunan rigakafi guda dubu a cewar Abdulaziz Abdullahi baban jami'i a hukumar lafiya ta kasar. Ya kara da cewar wannan gudumawa da suka karba za su rabawa ma'aikatan asibitoci da ma dakunan gwajegwaje.

Masana a fanin lafiya tuni sukai ta nuna damuwar su a kan Najeriya kasancewar kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka da kuma fanin lafiyar ke cikin mahuyacin halin.

Jack Ma ya taimakawa duk kasashen Afirka 54 a wannan lokaci da duniya ke cikin mawuyacin hali.