Iyaye na gudun rigakafin yara a Ostareliya da Amirka
April 12, 2015Talla
Firaministan kasar Ostareliya Tonny ya bayyana a yau Lahadi cewa kasar za ta fidda tsarin sanya shinge ga cin moriyar gwamnati ga iyalan da suka ki amincewa 'ya'yansu a yi musu allurar rigakafi.
Wannan tsari na zuwa ne bayan da ake samun iyalai da dama a kasar da basa bari a yi wa 'ya'yansu allluran rigakafi wacce suke cewa tana da hadari ga lafiyar 'ya'yansu.
Wannan yukunuri dai na zuwa ne adaidai lokacin da ake samun bullar cutar kyanda wacce ke da rigakafi a wasu daga cikin kasashen Turai da ma wasu sassan Amirka.
Fiye da yara 39,000 ba a yi musu allurar rigakafin ba a kasar ta Ostareliya.