1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a zirin Gaza

March 26, 2024

A daidai lokacin da mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka cimma matsaya kan bukatar gaggauta tsagaita bude wuta a zirin Gaza, dakarun sojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a birnin Gaza da Rafah.

https://p.dw.com/p/4e8jh
Sojojin Isra'ila a harabar asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.
Sojojin Isra'ila a harabar asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.Hoto: Victor R. Caivano/AP Photo/picture alliance

Tun daga daren jiya litinin 25 ga watan Maris 2024, zuwa wayewar gari Isra'ila ta yi ta kai hare-hare babu kakkautawa a yankin da kimanin mutane sama da milyan daya suka nemi mafaka a shiyyar asibitin Al Shifa.

Palästinensische Gebiete Gaza-Stadt Al-Shifa Krankenhaus
Hoto: Mohammed Ali/XinHua/dpa/picture alliance

Karin bayani: Bin Salman ya bukaci tsagaita wuta a Gaza

A yankin arewacin Gaza, guda daga cikin iyalan Hassera ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sojojin Isra'ila sun shafe kusan dukkan zuri'arsu daga doron kasa tare da kashe dubban mutane a yankin na asibitin Al-Shifa.

Karin bayani: Yakin Gaza: Sakatare Janar na MDD na ziyara a Masar

Sabbin hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya cimma matsayar bai daya a karon farko na bukatar gaggauta tsagaita bude wuta a zirin Gaza, kudurin da Amurka ta ki kada kuri'a kan gaza amincewa da daftarin da ta gabatar kan bukatar tsagaita wutan.

Karin bayani: Yakin Gaza ya haska nasarar Trump da Biden a Michigan

Ma'aikatan lafiyar Gaza ta sanar da sabbin alkaluman Falasdinawan da suka mutu a yakin na Gaza da adadinsu ya zarta dubu 32,414 galibinsu mata da kananan yara.