1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Isra'ila ta dage kan afkawa Rafah

March 17, 2024

Isra'ila ta yi watsi da kiraye-kirayen kasashen duniya kan hadarin da ke tattare da shirinta na afka wa birnin Rafah da ke kundancin yankin Falasdinu a yakin da take da Hamas.

https://p.dw.com/p/4dp2k
Isra'ila ta dage kan afkawa birnin Rafah
Isra'ila ta dage kan afkawa birnin Rafah Hoto: Bassam Masoud/REUTERS

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa matsin lambar da kasashen duniya ke masa ba za ta hana dakarun kasar ba afka wa Rafah, birni daya tilo da ya rage wa al'ummar Falasdinu akalla miliyan daya da rabi da yakin ya raba da matsugunensu.

Karin bayani: Isra'ila za ta afka wa Rafah cikin Ramadan

A yayin wani taro da ya gudanar da jami'an gwamnatinsa a ranar Lahadi, Mista Netanyahu, ya ce babu gudu babu ja da ja baya a game da alwashin da ya dauka na karya lagon kungiyar Hamas ta hanyar kutsawa birnin Rafah domin fatattakar ragowar mayakan kungiyar.

Karin bayani: Hamas ta gargadi Isra'ila a kan shiga Rafah 

A ranar Asabar da ta gabata, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya roki Isra'ila da ta jingine wannan shiri na kaddamar da farmaki a birnin Rafah don jin kan al'umma.