1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta afka wa Rafah cikin Ramadan

Abdullahi Tanko Bala
February 19, 2024

Isra'ila ta ce za ta kai hari Rafah a farkon Azumin watan Ramadan idan Hamas ba ta sako ragowar mutanen da ta yi garkuwa da su ba.

https://p.dw.com/p/4cZo2
Takaicin mutuwar dangi a Rafah
Hoto: MOHAMMED SALEM/REUTERS

Isra'ilar dai ta yi biris da matsin lambar da kasashen duniya ke yi mata na kare rayuwar Falasdinawa fararen hula da suka nemi mafaka a kudancin birnin Rafah.

Wani dan majalisar gudanarwar sra'ila Benny Gantz ya yi gargadin cewa sojojin Israila a shirye suke su danna zuwa cikin Rafah.

Karin Bayani: MDD ta bukaci da a dakatar da Isra'ila daga kai hari a Rafah

Kasashen duniya na nuna damuwa kan makomar Falasdinawa miliyan daya da dubu dari hudu wadanda Isra'ila ta tilasta musu zuwa Rafah daga kan iyakar Masar inda suke fuskantar hare hare da karancin abinci da kuma cunkoson wurin zama.

Ko da a ranar Lahadi farmakin da Israila ta kai cikin dare a Gaza ya hallaka Falasdinawa fiye da 100 yawancinsu mata da kananan yara wanda ya kai adadin mutanen da suka rasu zuwa fiye da mutum 29,000 a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Falasdinawa.